Hamisu Breaker - Ina Nazari paroles de chanson

paroles de chanson Ina Nazari - Hamisu Breaker



(Suiter on the beat)
Ina nazari, nifa kamar so yayi mini illa
Ki lura dani, ko zan warke watakila
Kece sanadi, wasu ke mini kallon gaula
Suke zunde na ni kuma ban iya ce masu kala
Ban son ki tafi, ni ban son ki mini bankwana
Yadan kadafi, so naki ya kama maganai na
Ya hanani sukuni, kar ki bari a ji kuka na
Ki yarda dani, ki fura ni ki saya asirai na
Komai kika ce ni bazan ki na amshi bukatu ba
Bazan iya cutar dake inyi wa kai na ba
Ni banga abin da zaki min bazan hakure ba
Ki so ni kawai na baki dama ban janye ba
Yarda da masoyi, yarda tushen kauna
Ki gane ina yi, so naki na damu na
Bangane sanyi, kuma ni ban gane zafi
Bangane kai na, dafin so ke mini zafi
Ina ta bulayi, jiki na yau ba karfi
Abinda nake ji, in zana kwatanta yafi
Ki tarbe ni, kin ga inai miki so bisa gaskiya
Ki kalle ni, kin ga wasika ce budaddiya
Ki sabe ni zaki ji tsantsar sirrrin zuciya
Kika karbe ni ko toh kauna ta zauna lafiya
Kiyi mini rumfa na fake a gari nasu kauna
Duk yanda kike so na tsaya ko kuma na tsugunna
Ki daina tunanin nima zan yaudari kai na
Bazan saba miki ba, in kin zama mai daki na
Kawai muyi soyayya
Kuma kar muyi jayayya
Akai naki na shirya
Kuma bana ja baya
Ina da farar aniya
Farar aniya laya
Kinai mini alkunya
Irin na masoya
(Suiter mix)




Hamisu Breaker - Ina Nazari - Single
Album Ina Nazari - Single
date de sortie
27-03-2024




Attention! N'hésitez pas à laisser des commentaires.