Nura M. Inuwa - Dan Almajiri paroles de chanson

paroles de chanson Dan Almajiri - Nura M. Inuwa




Kuyi kiran 'dan almajiri
Almajiri, yana bara, ga 'dan almajiri
Umm na 'dau 'koko na zanaje bara
Ku tausaya mani 'dan almajiri
Kuyi kiran 'dan almajiri
Almajiri, yana bara, ga 'dan almajiri
Na 'dau 'koko yau ina bara, domin neman abinda zanaci
Nai ankara, lallai komai, na duniyar ga baida tabbaci
Kukan tsun-tsu, cikin dawa, zance yake namaku tsokaci
Mai gaskiya, a magana, yau shi yake zama makaryaci
Da wahala samun nagari
Um Almajiri, yana bara, ga 'dan almajiri
Mai shirin sallah, yai alwala, kafin tazo ta wuce lokaci
Guna yunwa, tayi yawa, tasanya na fita a hayyaci
Na gigice, Kuma na rame, banda kuzari, kamar matsoraci
Ni kunga bara, dole tazaman min, tasa nazam abin kwatankwaci
'Kara kirana Almajiri
Almajiri, yana bara, ga 'dan almajiri
Ku tausaya mana, ku taimaka mana
Ku bamu na Allah ku bamu na annabi bayin Allah
Kuyi kiran 'dan almajiri
Almajiri, yana bara, ga 'dan almajiri
Da uwa da ubana, a duniya, da zanbi nida wanda baida su
Su sunyi gabas, ni nai yamma, yaushe haduwar mu tinda munka so
Ko dabarar, wacce nake, a sandinsu ne ta assasu
Mu ke yawo, lungu sako, kokan hanya ka ganmu munka so
Mune madaukin attajiri
Almajiri, yana bara, ga 'dan almajiri
Bayin Allah, ku taimaka, ku tausayawa 'dan almajiri
In kunsamu, Kuma kun bamu, mun tsira bamu 'kara yin jiri
In kun hana, kun kyare mu, to zamuje mudinga gararari
Kaji 'kan na 'kasa, wanda ke a sama, to shidai ma farkon shi jinjiri
'Yan uwana mui zikiri
Almajiri, yana bara, ga 'dan almajiri




Attention! N'hésitez pas à laisser des commentaires.