Hamisu Breaker - So Dadi Lyrics

Lyrics So Dadi - Hamisu Breaker



(Su-su)
In ba, in ba, in ba, in baka soyayya ja da baya
Ni na fadi ina dadawa
(Sultan with the beat baby)
So yanai mini dadi
Zo ka kalli jiki na
In ka kalli jiki na zaka gane so ya gamai mini rana
Ni nake zance, fahimta ce so na dauka a farko
So jakada ne shi
Ina nufin gun maza har mata
In baka soyayya ja da baya
Don mukam wa shi muke biyayya
Duk mai yin so kar ya sanya karya
Sai mun tashi zamu jinjina wa soyayya
In baka soyayya ja da baya (ni na fadi ina dadawa)
Don mukam wa shi muke biyayya (ba don so ba yanzu babu kowa)
Duk mai yin so kar ya sanya karya (so yabi jikin mu)
Sai mun tashi zamu jinjina wa soyayya
Nayi aniyar in gai da sarki
Sarkin da ba'a cin shi da yaki
Sa mamaki dole kanwa ga naki
Tun farko kai ne kuma gashi karshe ma haka
Ni in banda so bana da komai
Duk abinda zai saka ni zan mai
Nifa a kan shi zana iya komai
Indai bai saba wa Rabba na ba so zan maka
Kamar wasa na gani
Ina bin sa yaje dani
Ya dauke ni ya lula ni
Yau gashi yanai dani
Kan shi an min lamunin in fadi
So ba wasa ba, hayye
So ba wasa ba, hayye
So ba wasa ba, hayye
So ba wasa ne ba
Duk wanda yace ma baya soyayya
Zance ne dan dole zai biyayya
Da zarar yayi adashen wata shiyya
So dole ne na fada
Wanda zaya karyata ya tambayi na gaban sa




Hamisu Breaker - So Dadi - Single
Album So Dadi - Single
date of release
27-03-2024




Attention! Feel free to leave feedback.