Nura M. Inuwa - Soyayya paroles de chanson

paroles de chanson Soyayya - Nura M. Inuwa




Soyayya ruwan zumace
Yara kusha kubai masoyi
Yau da gobe naga Allah don haka duniya tabawa
Eeeee
Soyayya ruwan zuma
Wasuko sukace ruwan gubace
Wasu ta dagasu amma ga wasu ta agesu kwance
Wasu sunyi arziki sanadi nata wassu nata rance
Wasu sammako sukema wasu suyo fitar maraice
Wasuma gudu sukeyi tunda shigarta matsalace
To akanta ya akene gata jikin yaro da babba
Soyayya ruwan zumace
Yara kusha kubai masoyi
Yau da gobe naga Allah don haka duniya tabawa
Ee wasusun riketa sosai soyayya ai ni'imace
Itake batar da laifi wanda akaiwa ya makance
Wasu sunyi nasara wasuko agurinsu kaddarace
Wasu riba suka irga
Wasu asara sukayi zance
Haka baisa sukasa komawa so baya suka mance
Wanda zayyi ban hanashi don gargadi bazai jiyaba
Soyayya ruwan zumace
Yara kusha kubai masoyi
Yau da gobe naga Allah don haka duniya tabawa
Ee haka daidai fadi tashi irin tafiyarmu ta kasance
Yanayi irinna cutar soyayya bata tunzurace
Ita keraba mutum da mutane yaita san kadaice
Yaita zaro magana arashinasa ni danya dimauce
Uzuri zana yimai shine daidai ko ahunce
Wanda dukka yayyi nisa kunga kira bazai jiyaba
Soyayya ruwan zumace
Yara kusha kubai masoyi
Yau da gobe naga Allah don haka duniya tabawa



Writer(s): Farouk M Inuwa, Isa Gombe, Mubarak Dutse, Rr


Attention! N'hésitez pas à laisser des commentaires.