Nura M Inuwa - tsananin rabo Songtexte

Songtexte tsananin rabo - Nura M. Inuwa

Ni tsananin rabo ne ya fito da masoyiya ta
Na fada maki, haka so yake, a gareki na 'karaso
Tsananin rabo na ya hada ni da Sahibi na
Sona kake, haka na rike a gareka na 'karaso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Ehh tsananin rabo na tare dani kaine
Matsayinka zuciya babban sahibi ne
Ka samu gu a cikin raina ka zaune
So ba fada, zo nama rada, kaji zantuka na naso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Eh 'dan dakata labari zana baki
Dan garkuwa fuskarka ta nuna shauki
Nayo mafarki wai mun zauna a 'daki
To ana haka, sai na wartsaka, ba wanda zaimin iso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Eh sona a rana yafada wuya a huta
Kaine kaidai nake ta tinani karka manta
Inzaka je masallaci zan baka buta
Ba pallasa, sone yasa, zan bika fada taso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Eh duk inda so yake tare suke da 'kauna
Wanne kike mani 'dan juyo mu gana
Nidai gabadaya sirri na na tona
Na fada maki, mizan rike maki, baya na kalma taso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Eh mezan fadama sai ka mallake ni
Jiki na saki duk inda kaso kajani
Sharadi naso bai duban kyau kokwa muni
Nai bankada, ba war-wara, wazai gane fuska taso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Eh so bai fado da kwatance ko misali
Ba'a yimar tuhuma ta shiga dalili
Indai ka tsincin kanka a ciki ka taka 'kulli
Sai rayuwa, tayi ginuwa, ni ina cikin gida naso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso
Eh tsananin rabo ne ya fito da masoyiya ta
Na fada maki, haka so yake, a gareki na 'karaso
Tsananin rabo na ya hada ni da Sahibi na
Sona kake, haka na rike a gareka na 'karaso
Sanadin rabo in yazo da wuya ya koma
Asali na so, gado mukai, a jikin mu ya pallatso

Attention! Feel free to leave feedback.