Nura M. Inuwa - Kai Da Kai Songtexte

Songtexte Kai Da Kai - Nura M. Inuwa

Kai da kai kuke a cikin rai na
Kun zamo 'daya, wazana bari wazana 'dauka
Cikin ku babu nayarwa
Kai da kai muke a cikin ranki kisani
Taura daya baki biyu bai taunawa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
Ku duba na kamu da sanku (kai da kai)
Zuciya ta na begen ku (kai da kai)
Dayake ba bare acikin ku (kai da kai)
Nida kai so da 'kaunar mu nayo karbewa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
Nida ke sanki taho kiji zance (kai da kai)
So yai tsanani ya zarce ayo kwatance (kai da kai)
Ki aminta dani mu kasance (kai da kai)
A guri 'daya mu kasance kasance ba rabewa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
To gamo na jini gashi yau na kamu (kai da kai)
Soyayyar mu tai mani kamu (kai da kai)
Da kamar wasa so ya somu (kai da kai)
Gashi zai zama ciwo maiyin firgitarwa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
Gunki nine zan zama gwani (kai da kai)
Kan sanki nakeyin tunani (kai da kai)
Sanki ni shiyaka tsumani (kai da kai)
Kaida kai ki daina hada mu ki banbantawa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
Gani a cikin tarko nagaza fita (kai da kai)
Bada danganci nai kurubuta (kai da kai)
Zuciya ta ban iya saita ta (kai da kai)
Ku biyu a cikin rai kun zama mafakar fakewa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
Umm ni ya kamata nazama zabinki (kai da kai)
Tauraro mai haske ruhinki (kai da kai)
Kaga fuskar ki nayi sheki (kai da kai)
Haske ya bayyana idonki kiyo budewa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa
Kai da kai kuke acikin raina
Kun zamo 'daya, wazana bari wazana 'dauka
Cikin ku babu nayarwa
Kai da kai muke a cikin ranki kisani
Taura daya baki biyu bai taunawa
Kai da kai kuke so ya hadawa
Ku zame 'daya taurari biyu kuke haskenku baya dishewa

Attention! Feel free to leave feedback.