Nura M Inuwa - auren masoya aminu da khadija Songtexte

Songtexte auren masoya aminu da khadija - Nura M. Inuwa

Eh auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Ni farko nasanya sarki Allah mai juya zamani (mai dadi)
Sarkin da yai Ummi a gareni kuma yayi ni (mai dadi)
A gareni hassada na mutanen wanga zamani (mai dadi)
Ka yarda dai na wake amare gunsu soyayya tai dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Ayo duhun salati a gurin Mahamudu manzonka (mai dadi)
Da Alihi dasa sahabbai masu biyarsa ba shakka (mai dadi)
'kauna da sansa cikin raina ni Nura yai suka (mai dadi)
Sainna kira sunansa araina sannan nake jin dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Eh aure na soyayya aka 'daura mu muna murna (mai dadi)
Munzo gurinsu amarya da ango dan tayan murna (mai dadi)
Ranar farinciki ce dangi kufito ku 'dan nuna (mai dadi)
Aure na soyayya Aminu Khadija kui takon fadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Eh Khadija kinyi dace da Aminu dan yana sanki (mai dadi)
Mun tabbata hakika dukanin hakkun ki zai baki (mai dadi)
Zaman gudan aure to sai kizamo gwanar girki
Jimai yakeso ki masa donin kedashi zama yai dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Eh dayashigo gida tashi kizo ki tarbe shi (mai dadi)
Udan yana fushi taso zo ki taushe shi (mai dadi)
Komai tsanani kada yazam har kinci alwashi (mai dadi)
Kinji ki hakan da kikeyi kinkaji ko ba dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Eh komai yake bida a gareshi yazam kina yimai (mai dadi)
Da ya bukaci ruwan wanka sai kice mar (mai dadi)
Kafin ya fito abinci a ajere ki kaimai (mai dadi)
Yaci yai murna da abin kikai mai dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Kaima Aminu tashi da sauri zan kirawo ka (mai dadi)
Khadija ta zama matar ka nauyi nata ka 'dauka (mai dadi)
Kazam mai kula da ita domin kuyo harbi (mai dadi)
Acikin auren da kukai da ita auren ku yazam mai dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Acikin aure kaida ita to kar ka cuce ta (mai dadi)
Dan wajibi a gareka hakki nata ka bata (mai dadi)
Kuyo zama 'kalau to karda takai ga zalunta (mai dadi)
Sannan in kuka hadu sai kaga zama yanayin dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Aurenku dukkanin dangi kowa yana murna (mai dadi)
Iyaye na ango dukkanin su na murna (mai dadi)
Yayye da 'kanne ku tsaya sunan su zan zana (mai dadi)
Ku nai wakewa domin rana ce mai dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi
Mai dadi
Mai dadi
Mai dadi
Auren masoya an 'daura mu muna murna
Sannu Aminu ango gurin Khadija kuyo zaman lafiya mai dadi

Attention! Feel free to leave feedback.