Nura M Inuwa - da kalaman so Songtexte

Songtexte da kalaman so - Nura M. Inuwa




Eh da kalaman so kika jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoki raka ni
Eh da kalaman so kaja jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoka raka ni
Um indai har kinka hana kallon kallo da bayani
Ni naimaki babu dalili amma na kasa sukuni
Zuciya ta tagaza 'daukar zancenki yana rudani
Saurari abinda ta 'dakko
Maganar ki tayo saita ni
Da kalaman so kaja jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoki raka ni
Eh da zuwa kajani da sauti harma na baka mukami
Doka ta yau ka karya fili nai maka mukami
Lallai ka koren shakka kai zaka ciken wani mukami
Likin so zai warkewa
Kan siddi ka 'daura ni
Da kalaman so kika jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoka raka ni
Rai baya jure rikon so in yazo dole a furta
Sirrinna cikin 'kirjina na bude sai ki karanta
Ga amanar kai na baki mai sona karda ki manta
Tseren sukuwa nai sauri
Dokin 'kauna ya zigani
Da kalaman so kaja jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoka raka ni
Da kalaman so kika jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoki raka ni
Eh inka sauko zan zauna wannan shine lissafi
Ladabi da biyayya tsani banayin hanyar rafi
Magana 'daya zanayi 'karshe so ko 'daya bashida laifi
In mun auren mu a 'daki
In zani wuri ka rakani
Da kalaman so kika jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoka raka ni
Kin kaini wajen da nike so zance shi zana tayaki
Innayi 'barin zance ne ki fada man na saki baki
'Kwa'kwalwata na aiki kin sani inata mamaki
Na baki bayani kanso
Kalmar 'kauna kika bani
Da kalaman so kaja jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoki raka ni
Eh tuta kowa ke nuni ga tawa ta so zan nuna
Da kudi kowa ke jari ni so ya zamo jarina
Fara'arka na ganinda fuska 'karkon sirri na
Ka rikeni amana kardai
Wahala tasaka ka kabarni
Eh Da kalaman so kika jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoki raka ni
Da kalaman so kaja jani hanya na kasa ganewa
Mai sona zoka raka ni




Attention! Feel free to leave feedback.