Nura M Inuwa - Mai Mage Songtexte

Songtexte Mai Mage - Nura M. Inuwa




(Mai mage)
(Mai mage)
Tafiyar tayi baza'a kada dakai ba (Mai mage)
Bishiyar dogon yaro tayi timber (Mai mage)
Mai rayaman gidan mu ware tsaba (Mai mage)
Gun nagarta ba"a san kamar yakai ba (Mai mage)
Mun amince (Mai mage)
Kayi zarce (Mai mage)
Ka 'ki sabo guda bare a da yaji (Mai mage)
Damusa zafina kadai a daji (Mai mage)
Baka tsoro bare a saka kundi (Mai mage)
Kai 'kafa ne ka saba taka birji (Mai mage)
Munyi adabo (Mai mage)
Da masu zanbo (Mai mage)
Kazamo saiwa assali na reshe (Mai mage)
Ginshiki ne kai na fada da harshe (Mai mage)
Banda ungulu me za ayo da reshe (Mai mage)
Ko ginin 'karya dole ne ya rushe (Mai mage)
Innuwa ne (Mai mage)
Gun mutane (Mai mage)
Ita 'kaya kowa hauta zaiyi sartse (Mai mage)
Mai nema mai gyada yaje ya matse (Mai mage)
Na bisan hanyar zaki sai ya ratse (Mai mage)
Alfijir ya keto gari ya haske (Mai mage)
Kunji 'kwaro (Mai mage)
Mai fasa taro (Mai mage)
Shikaba jama'a jari suyi sana'a (Mai mage)
Kuma yai fatan Allah bada sa'a (Mai mage)
Ku matasa kuzo mu nuna 'da'a (Mai mage)
Honourable mai mage yana da fara'a (Mai mage)
Mai hasashe (Mai mage)
Babu kushe (Mai mage)
Naka kamar katapila fage na aiki (Mai mage)
Shinga manya gona a sanya taki (Mai mage)
Mai yawan kuka shi yakeda raki (Mai mage)
Ga chairman da baya tauye hakki (Mai mage)
Yayi rumfa (Mai mage)
Ta kore jarfa (Mai mage)
Ni farar aniyana na kirata laya (Mai mage)
Wanda ke farko ya wuce na 'kurya (Mai mage)
Mai fada aji shi zaya 'daga murya (Mai mage)
Bani in baka yazamo musanya (Mai mage)
Nai kwatance (Mai mage)
Ya kasance (Mai mage)
Nesa tazo kusa al'ummar garinmu (Mai mage)
Kunga dama bamuso tabarmu (Mai mage)
Shawara ta kar mu yada namu (Mai mage)
Wanda ke nema zayaso ya samu (Mai mage)
'kuri'a ta (Mai mage)
Zan saka ta (Mai mage)
Jam'iya mai mage da basu sata (Mai mage)
Shikwa 'bera baya gudun 'karanta (Mai mage)
Innda duk ka tsaya gaskiya ka furta (Mai mage)
Yara manya kuzo mu 'dauki tuta (Mai mage)
Nai kiranmu (Mai mage)
Mu hada kanmu (Mai mage)
Lokaci yayi kar muje mu zauna (Mai mage)
'kurri'arka ka dangwala ka nuna (Mai mage)
Na fada nidai mage ne gwanina (Mai mage)
Dankwa nasanshi ya'darar da saura (Mai mage)
Shi kuke so (Mai mage)
Yafi kwanso (mai mage)
Shi hali abokin tafiya ne (Mai mage)
Kama da wane bata baka wane (Mai mage)
Mai 'kwa-'kwalwa yake gani y gane (Mai mage)
Damu dakai honourable muna a jone (Mai mage)
Mu gudu tare (Mai mage)
Mu tsira tare (Mai mage)




Attention! Feel free to leave feedback.